Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila biyu sun ji rauni a wani hari da wuka a yankin Atirat na arewacin Ramallah, a yau talata kuma sojojin sun kashe maharin.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe maharin bayan lamarin. Sanarwar rundunar ta ce:
"Sojojin sun isa wurin ne bayan sun sami rahoton wani mutum da ake zargi kusa da garin Atirat."
"A lokacin binciken, mutumin da ake zargi ya kai hari kan sojojin, wadanda jami'an suka harbe nan take"
An bai wa sojojin biyu da suka ji rauni taimakon lafiya, kuma maharin yayi shahada.
Zuwa yanzu, babu wani rahoto mai zaman kansa game da lamarin da ya fito daga shaidun Falasdinawa.
Your Comment